Thursday, December 12, 2024

WAKAR SAMANIYA

                                                         Domin Murtala Uba

Can take bisa kawunanmu

Sai mun xaga kai da idanuwanmu
Ta yi qoli, ba mai iya sa gannanmu
Su hango ina ta kare daga lungunnanmu

Ita ce xauke da iska don mu shaqa
Daga gareta rana ke haska mu ba mushaqqa
Hadari da girgije na nan kowace kiqa
Halitta ce ta Mafi zalaqa

Sama, ba wasa aka yi ta
Ta wuce duk tunani na fahimta
Babu sanin iyakacinta
Sai Allahu da yake halinqinta

Ga duniyoyi ko’ina an aje su
Ga taurari gari-gari aggaresu
Kai, ko yula da mashi Ya saka su
Kowane na bin umarnin Ubangijinsu

 

Allahu Mai halitta ba irinsa
Ikonsa ya fi tunanin halittarsa
Qarfinsa ya wuce ai musunsa
Huwallazi wanda babu irinSa.

No comments: